
Ɗan Majalisar Wakilai ta Taraiya mai wakiltar mazaɓar Wurno/Rabah, Ibrahim Al-Mustapha ya baiyana ƙwarin gwiwa cewa jam’iyar APC ce za ta kafa mulki a Jihar Sokoto a 2023.
Al-Mustapha a yau Litinin a Abuja ya shaida wa kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN cewa “Sokoto jihar APC ce”.
“Kawai dai ƙaddarar siyasa ce ta sanya APC ta rasa Sokoto. Amma ina mai tabbatar da cewa waɗanda su ke PDP ma za su dawo APC kwanan nan.
“In Allah Ya yarda, idan 2023 ta zo, APC ce za ta kafa mulki a Sokoto,” in ji shi.