
Jam’iyyar APC ta kori jami’in yaɗa labaranta na Jihar Anambra, Okelo Madukaife sakamakon taya Farfesa Charles Soludo murnar lashe zaɓen gwamna da ya yi a jihar.
Shugaban jam’iyyar na jiha, Basil Ejidike, a wata ganawa da manema labarai a ranar Lahadi ya baiyana cewa Okelo ba shi da ikon yin magana a madadin jam’iya sabo da an riga an dakatar da shi tun a watan Yuni sakamakon zargin laifin maƙarƙashiya.
Ya ƙara da cewa “tun a Yuni mu ka dakatar da Okelo sabo da yana ɓatawa jam’iyar mu suna, sabo da haka bashi da damar da zai zo ya yi magana a madadin jam’iya.
“Bayan an dakatar da shi, sai ga shi kuma ya shiga rediyo ya na cewa ya na bayani ne a madadin jam’iya. To gaskiya hakan bai mana daɗi ba, kuma mu ba za mu yadda da hakan ba,”
Madukaife ya ƙara da cewa, “tun a watan Yuni da a ka dakatar da Okelo ya ke zagi da ci mana mutunci. Bari ma na sanar da ku cewa tun wannan lokacin baya halartar taruka da sauran harkokin jam’iya,”
Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan jam’iya da ƴan jarida da sauran al’umma da su dena hulɗa da shi a matsayin ɗan jam’iyar APC, in da ya ce, “mu a wajen mu, Okelo ba ɗan APC bane.”