Home Labarai APC ga Kwankwaso: Ba a bar rabon tallafin abinci a hannun gwamnatin NNPP ba saboda gudun handama da babakere

APC ga Kwankwaso: Ba a bar rabon tallafin abinci a hannun gwamnatin NNPP ba saboda gudun handama da babakere

0
APC ga Kwankwaso: Ba a bar rabon tallafin abinci a hannun gwamnatin NNPP ba saboda gudun handama da babakere

Jam’iyyar adawa ta APC a jihar Kano, ta soki Dakta Rabi’u Kwankwaso, jagoran jam’iyyar NNPP, bisa sukar da ya yi wa tsarin rabon tallafin kayan abinci da gwamnatin tarayya ta yi.

A cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC na jiha , Abdullahi Abbas ya fitar, ya ce gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar rage yunwa a kasar nan, amma gwamnatin NNPP a Kano na kawo cikas ga wannan ƙudirin.

Ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da wasu matakai na tallafawa marasa galihu da marasa karfi amma wadanda aka ba su don raba wa al’umma a Kano na karkatar da kayan

Abbas ya ba da misalai da yadda ake zargin wasu manyan jami’an gwamnatin NNPP da hannu wajen karkatar da kayan abincin.

Shugaban jam’iyyar ta APC ya yi kira ga Kwankwaso da ya umurci gwamnansa da ya binciki wadannan abubuwan da suka faru tare da tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan aika-aika sun yi girbi abinda su ka shuka a kotu.

Ya kuma soki Kwankwaso da cewa ba a hannun APC kadai aka bar aikin rabon ba.

A cewar Abbas, kwamitin da gwamnatin tarayya ta sake kafa wa ya hada da mambobin jam’iyyun siyasa daban-daban da suka hada da NNPP da PDP da kuma IPAC.