
Jam’iyyar APC mai mulki ta buƙaci Ministan Kwadago da samar da Aikin-yi, Chris Ngige da ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar, Bola Tinubu ko ya ajiye muƙamin nasa na minista.
Mataimakin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na kasa, Murtala Ajaka ne ya faɗi hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
A sanarwar, Ajaka ya bukaci ministan na kwadago da ya yi murabus idan har ba zai iya fitowa fili ya goyi bayan dan takarar shugaban kasar na.
Ministan na kwadago, a yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels TV, Politics Today a ranar Juma’a, ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, ya na mai cewa zai nuna goyon bayansa ne a akwatin zaɓe.
Da mai gabatar da shirin ya matsa masa lamba kan ya bayyana dan takarar da yake so tsakanin dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi, da dan takarar jam’iyyar APC, ministan ya ce tambaya ce mai wahala, inda ya bayyana mutanen biyu a matsayin abokansa.
Sai dai a sanarwar Ajaka ya ce abin takaici ne ga Ngige, wanda ke rike da mukamin minista a gwamnatin APC, ya yi irin wannan maganar.
Ya kara da cewa duk wadanda ke riƙe da muƙamai, dole ne su ajiye bukatarsu a gefe su yi kokarin ganin jam’iyyar ta APC ta samu nasara ko kuma su ajiye muƙaman.