
Zaɓen Shugabannin Jam’iya na Ƙananan Hukumomi ya ƙara ta’azzara rikicin da ke jam’iya mai mulki ta APC a Jihar Zamfara.
Rahotanni sun baiyana cewa zaɓen ya sanya APC ta rabe gida uku, inda kowanne ɓangare ke iƙirarin cewa shine halastacce a jam’iyar.
Ɓangarori ukun sune na gwamna mai ci, Bello Matawalle, wanda tsohon gwamnan jihar, Ahmed Yarima ke goyawa baya, sai ɓangaren tsohon gwamna, Abdul’aziz Yari sai kuma na Sanata Kabiru Marafa.
Da ya ke jawabi a jiya Asabar, Matawalle ya yi kira ga duka ɓangarorin da su maida wuƙar su dawo a haɗe kai domin ciyar da jihar gaba.
Matawalle ya yi wannan kira ne a Sakateriyar Ƙaramar Hukumar Maradun, inda ya ke ganawa da wakilan zaɓen na ɓangaren sa bayan ya yi zaɓen, inda man ce mahaifarsa.
“Ni har yanzu a gani na APC ɗaya ce a jihar nan tunda har yanzu babu wata kotu ko uwar jam’iya da ta ce a dakatar da zaɓen shugabannin jam’iya.
“Kasancewar babu waninumarni daga kotu ko uwar jam’iya ta ƙasa kan a dakatar da zaɓen jam’iyar, to hakan ya nuna cewa lallai zaben halastacce ne,” in ji Matawalle.
Gwamnan ya kuma zargi wasu daga cikin ƴan jam’iya da yaudarar wasu daga ciki har su ke sukar shugabannin jam’iyar a jihar danna ƙasa baki ɗaya.