
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, a jiya Alhamis ya fasa ƙwai, inda ya ce matakin cin hanci da rashawa a karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na kwamitin riko da tsare-tsare na musamman ya kazance.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Adamu, wanda ya bayyana haka a wata tattauna wa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja, ya ce sun gaji basussukan kuɗi har Naira biliyan 7.5 daga kwamitin rikon kwarya da Buni ya jagoranta.
Akan dalilin da ya sa aka kori daraktocin sassa daban-daban a shelkwatar APC, Adamu ya ce matakin cin hanci da rashawa a tsarin da suke kai ya yi yawa.
Daily Trust ta ruwaito a ranar Alhamis din cewa Adamu ya maye gurbin daraktocin da ya dakatar tun da farko.
Adamu, a ranar 22 ga watan Afrilu, ya umarci dukkan daraktoci a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja da su tafi an dakatar da su bisa zargin cin hanci da rashawa.
Daraktocin su ne; Anietie Offong (Darakta, Jindadi da walwala); Bartholomew I. Ugwoke (Bincike); Abubakar Suleiman (harkokin kudi); Dr Suleiman Abubakar (Gudanarwa); Salisu Na’inna Dambatta (Yada Labarai); da Dare Oketade, ɓangaren sharia