
Jam’iyyar APC ta soke taron yakin neman zaben shugaban kasa da ta shirya yi a jihar Kano.
Sakataren kwamitin yakin neman zaben, James Faleke a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a jiya Alhamis, ya ce an soke taron da aka shirya yi a ranar 16 ga watan Fabrairu a Kano.
Faleke bai bayar da wani dalili na soke taron ba.
Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa matakin soke taron ba zai rasa nasaba da yanayin karancin takardun Naira da kuma man fetur da su ka jefa ƴan ƙasa cikin halin ƙaƙanikayi ba.