
A ƙalla ƴan jam’iyar APC 1, 868 ne su ka sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta PDP a Sakkwato.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar PDP na jihar, Malam Hassan Sanyinnawal ya fitar a Sakkwato a yau Alhamis.
A cewar MSanyinnawal, ƴan waɗanda su ka sauya sheƙar, ƴan kasuwa ne daga yankuna 10 a fadin jihar, inda shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Bello Goronyo ya karɓe su a jiya Laraba.
Ya ruwaito Goronyo, wanda ya samu wakilcin shugaban jam’iyyar na shiyyar Sakkwato ta tsakiya, Muhammad Dangoggo, yana tabbatar wa sabbin shiga jam’iyyar cewa za a kula da su daidai da waɗanda su ka tarar a jam’iyar.
Shugaban jam’iyyar PDP ɗin ya yi alkawarin baiwa sabbin ƴaƴan jam’iyyar kulawa ta musamman, yayin da ya yi kira gare su da su yi amfani da kwarewarsu a harkokin siyasa da kasuwanci don tabbatar da nasarar jam’iyyar a babban zaben 2023 mai zuwa.
Shima da yake jawabi, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP na jihar, Sa’idu Umar ya yi maraba da sabbin ‘ya’yan jam’iyyar, ya kuma yi alkawarin hada kai da dukkaninsu domin samun nasarar jam’iyyar.
Umar ya taya wadanda suka sauya sheka murna, yana mai cewa, “Shawarar da suka yanke ya nuna kishinsu na goyon bayan kyakkyawan salon shugabanci na Gwamna Aminu Tambuwal.”