Home Siyasa MI’ARA KOMA BAYA: Dan takarar gwamna na Labour a Kano ya dawo APC

MI’ARA KOMA BAYA: Dan takarar gwamna na Labour a Kano ya dawo APC

0
MI’ARA KOMA BAYA: Dan takarar gwamna na Labour a Kano ya dawo APC

Bayan ya fice daga jam’iyyar APC bisa zargin yi masa rashin adalci da kuma karya ƙa’idojin dimokuraɗiyya, ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar Labour Party, LP, Bashir Ishaq Bashir, ya yi watsi da takarar ta sa ya dawo jam’iyya mai mulki ta APC a jihar.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa jim kaɗan bayan tsayar da mataimakin gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamna na APC a Kano, sai Bashir ya fice da ga jam’iyyar bisa zargin yi masa rashin adalci da kuma ƙin biyayya da ƙa’idojin dimokuraɗiyya.

Daga bisani, sai ya sanar da sauya shekar sa daga APC zuwa LP, inda ya ce a nan ne ya ga cewa jam’iyya ce da ta ke da irin manufofin sa kuma ta na bin dimokraɗiyya yadda ya dace.

Sai dai kuma tun a ranar 21 ga watan Janairu, dan takarar gwamnan ya kaurace wa taron gangamin jam’iyyar LP ɗin a Kano tare da shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Mohammed Zarewa; kodinetan yakin neman zaben Peter Obi na jiha, Balarabe Wakili da; dan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Idris Dambazau.

Wata majiya da ke kusa da dan takarar ta tabbatar da sauya shekar ta sa da wasu jiga-jigan jam’iyyar LP zuwa APC a jiya Lahadi, inda ta ce babban dalilin da ya sa suka sauya sheka shi ne na ware manyan masu ruwa da tsaki a Arewa wajen yanke shawara da kuma rashin samun cikakkiyar alkibla kan maslahar Arewacin Nijeriya. .

DAILY NIGERIAN dai ta samu labarin cewa tuni Bashir ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC har sau biyu da kuma mataimakin ɗan takarar shugaban kasa, Kashim Shettima a Legas da Abuja, inda su ka amince da sharuddan sauya sheka.

A cewar wata majiya, dan takarar jam’iyyar LP ya amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC tare da yin alkawarin tara masa magoya bayansa a lokacin zaɓe mai zuwa.