Home Labarai An ƙara samun wani matashin wuta ta ja shi ya mutu yayin sata a taransifoma

An ƙara samun wani matashin wuta ta ja shi ya mutu yayin sata a taransifoma

0
An ƙara samun wani matashin wuta ta ja shi ya mutu yayin sata a taransifoma

 

 

Wa ni matashi da ba a tantance wanene ba kuma a ke zargin mai sata a taransifoma ne ya rasa ransa yayin da wuta ta ja shi bayan ya je yin sata a ƙaramar tashar rarraba wutar lantarki mai ƙarfin 500KVA ta Umuezerimpi a ƙauyen Umuatuegwu a yankin Okija na Jihar Anambra a jiya Lahadi.

Emeka Ezeh, Shugaban Kamfanin Sadarwa na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Enugu, EEDC, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a Enugu, ya ce wanda ake zargin ya je yin sata ne kan kadarorin kamfanin da misalin karfe 6 na safe.

A cewar Ezeh, marigayin ba shi kadai ya je yin satar ba domin abokan satar tasa sai su ka tsere bayan da su ka fuskanci wutar lantarkin ta kama shi, inda suka bar gawarsa da kayan aikinsu a wurin da lamarin ya faru.

Ya bayyana cewa an shigar da rahoto a hukumance a ofishin ‘yan sanda na Okija, domin yin cikakken bincike.

“An kwashe karafunan aikin da matashin da abokansa su ka tafi da su wajen satar. An ajiye gawar tasa a dakin ajiye gawa na babban asibitin Okija.

“Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da EDC ta fitar da rahoto kan wasu mutane hudu da ake zargi da aikata barna da aka kama a hanyar sadarwarta bisa zargin kai hari kan na’urorinta na lantarki.

Sai dai kakakin hukumar ta EEDC, ya bukaci jama’a da su sanya ido tare da lura da yadda ake ganin cewa ‘yan ta’adda sun yi kaca-kaca, suna kai hare-hare a cibiyoyin EEDC da kuma kawo cikas ga kwastomomi a yankin Kudu maso Gabas.