Home Labarai Ƙaramar Hukuma ta raba kekuna 75 ga ma’aikatanta a Adamawa

Ƙaramar Hukuma ta raba kekuna 75 ga ma’aikatanta a Adamawa

0
Ƙaramar Hukuma ta raba kekuna 75 ga ma’aikatanta a Adamawa

 

 

Karamar Hukumar Mubi ta Arewa a jihar Adamawa ta raba kekuna 75 ga wasu ma’aikatanta masu ƙwazo.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, Shugaban karamar hukumar, Alhaji Suleiman Yahaya ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Yola a yau Laraba.

Ya ce daga cikin adadin, 35 an mika su ga masinjoji da ma’aikatan shara, yayin da 40 aka miƙa wa ƙananan ma’aikatan da ke aiki a fadar mai martaba Sarkin Mubi, Alhaji Abubakar Ahmadu.

Ya bayyana cewa an yi hakan ne domin sauƙaƙa zirga-zirgar waɗanda suka ci gajiyar zuwa wuraren aikinsu, inda ya ce an ba su kekunan ne kyauta a matsayin hanyar sufuri.

Shugaban karamar hukumar, ya yi kira ga waɗanda su ka amfana da su yi amfani da keken a hankali, yana mai jaddada cewa za a faɗaɗa wannan alherin domin karbar karin ma’aikatan da su ka cancanci a karɓe su da irin wannan shiri.

Bulus Zamaya, shugaban ma’aikatan shara na ƙaramar hukumar ya bayyana hakan a matsayin abin a yaba, kuma babu kamarsa, yayin da ya yaba wa shugaban bisa wannan karimcin.

Ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar kekunan da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu domin tabbatar da hakan ta hanyar aiki tukuru da kuma biyayya ga kafuwar da aka kafa, yana mai jaddada shirin zai rage musu matsalolin sufuri.