Home Kasuwanci Ƙarancin dakon man fetur ne ya haifar da wahalarsa a ƙasa — IPMAN

Ƙarancin dakon man fetur ne ya haifar da wahalarsa a ƙasa — IPMAN

0
Ƙarancin dakon man fetur ne ya haifar da wahalarsa a ƙasa — IPMAN

 

Kungiyar Dillalan Man man fetur Mai Zaman kanta ta Ƙasa, IPMAN, ta dora alhakin karancin dakon man fetur da ake samu daga defo na Legas a dalilin da ya haifar da wahalar man da ake fuskanta a Abuja da sauran sassan kasar.

Shugaban kungiyar ta IPMAN, Chinedu Okoronkwo ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Litinin a Legas.

Okoronkwo ya yi magana kan yadda layukan mai ke sake dawowa a wasu sassan kasar nan, musamman a Abuja.

Ya ce yaƙin Russia da Ukraine ya kawo cikas ga yadda ake rarraba man fetur cikin sauki.

A cewarsa, a yanzu haka dillalan man da ƴan dakonsa na fuskantar wahalar ɗauko man daga defo zuwa wasu sassan kasar nan.

Ya ce: “Kudin da ake kashewa wajen sayen man dizel yayi matuƙar tashi, inda hakan ya ke janyo wa muna samun faduwa.

“A Hakim yanzu ba zai yiwu a cigaba da sayar da mai kan frashin famfo na N165 ba indai na a sake duba a kan farashin ba.

“Muna kira ga gwamnati da ta duba halin da ake ciki ta hanyar yin nazari kan farashin kayan ko kuma kawo mana tallafi ga dukkan dillalai domin kawo daidaito a harkar,” in ji shi

Okoronkwo ya yabawa gwamnati kan yadda ta biya ƴan kasuwa kuɗaɗen dako kawo yanzu, inda ya kara da cewa ya kamata a yi kokarin biyan basukan da su ke bi gaba ɗaya.