Home Kasuwanci Ƙarancin man fetur: Lita biliyan 2.3 mu ke buƙata ya isa rabawa ƴan ƙasa — NNPC

Ƙarancin man fetur: Lita biliyan 2.3 mu ke buƙata ya isa rabawa ƴan ƙasa — NNPC

0
Ƙarancin man fetur: Lita biliyan 2.3 mu ke buƙata ya isa rabawa ƴan ƙasa — NNPC

 

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC, ya ce ya na sa ran samun litar man fetur sama da biliyan 2.3 zuwa karshen watan Febrairu a ƙasar nan.

Ya kuma baiyana cewa yanzu haka lita biliyan 1 ne a ke raba shi ga ƴan ƙasa.

Babban Darakta mai kula da ɓangaren mai na cikin ƙasa, Adetunji Adeyemi, a yayin ganawa da manema labarai, ya ce lita biliyan 2.3 da a ke buƙata shi ne zai dawo da wadatar man da a ke samu a ƙasa na kwanaki 30, har ma a samu rara.

Ya kuma tabbatar da cewa man fetur ɗin da a ke siyar wa a gidajen mai a halin yanzu a fadin ƙasar nan ingantacce ne.

Adeyemi ya ƙara da cewa domin an bunƙasa da hanyarta rarraba mai a ƙasar nan, kamfanin ya kirkiro da yin aiki na awa 24 a defo-defo domin biyan buƙatar yan ƙasa.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen ganin an magance matsalolin da a ke fuskanta wajen safarar man fetur.