Home Labarai Ɓarawon da ya addabi magidanci da sata har ya saki matarsa bisa zargi ya gurfana a kotu

Ɓarawon da ya addabi magidanci da sata har ya saki matarsa bisa zargi ya gurfana a kotu

0
Ɓarawon da ya addabi magidanci da sata har ya saki matarsa bisa zargi ya gurfana a kotu

 

 

Ƴan sanda sun gurfanar da wani matashi mai suna Umar Sa’ad Dakatsalle a gaban Kotun shari’ar Muslunci da ke zaman ta a shelkwatar Hukumar Hisbah ta jihar Kano, bisa zargin sata da shiga gida ba bisa izni ba.

Tun da fari, a na tuhumar Dakatsalle da kwashe shekaru 4 yana shiga gidan wani mutum mai suna Nuraddin Iliyasu, ya na ɗebe masa kuɗaɗe da kayayyaki.

Hakan ne ya sanya har ta kai ga Iliyasu yana zargin matarsa, inda hakan ya sa ya sake ta. Sai yanzu s ka gane inda gaskiyar ta ke.

Ana zargin shi da satar kayayyaki da kuɗaɗe na kimanin Naira Miliyan 2 da Naira dubu 40, laifin da ya saɓawa sashi na 212 da 113 na kundin shari’a (SPCL).

Sai dai kuma wanda a ke ƙarar ya musanya zargin da ake masa.

Bayan musantawar ta sa, sai mai gabatar da kara ya roƙi kotu da ta basu wata rana domin gabatar da shaidu.

Daga nan ne sai alkalin kotun, Sani Tanimu Hausawa ya amince da roƙon na su, inda ya aike da Dakatsalle gidan yari har sai 4 ga watan 10 domin sauraren shaidu.