Home Ƙasashen waje Ɓarayin shanu sun kashe mutum 11 a arewacin Kenya

Ɓarayin shanu sun kashe mutum 11 a arewacin Kenya

0
Ɓarayin shanu sun kashe mutum 11 a arewacin Kenya

 

Ƴan sanda a arewacin Kenya sun bayyana cewa aƙalla mutum 11 suka rasu, ciki har da jami’an tsaro takwas a wani harin kwanton ɓauna da ɓarayin shanu suka kai.

Wani basaraken gargajiya na daga cikin waɗanda harin ya rutsa a ranar Asabar a yankin Turkana.

Wata sanarwa da ƴan sanda suka fitar sun alaƙanta harin da hari na matsorata.

Dama a ƴan kwanakin nan jami’an tsaro na ta bin diddiƙin wasu ƴan ƙabilar Pokot waɗanda tun da farko suka kai hari a wani ƙauye suka sace shanu.

Ko a watan da ya gabata sai dai Shugaba William Ruto na ƙasar ya yi alƙawarin kawo ƙarshen ƴan fashi a arewacin Kenya.

 

BBC Hausa