Home Siyasa Ƴan Arewa na sayar da PVC ɗin su Naira 2000, in ji NEF

Ƴan Arewa na sayar da PVC ɗin su Naira 2000, in ji NEF

0
Ƴan Arewa na sayar da PVC ɗin su Naira 2000, in ji NEF

Kungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta yi zargin cewa ƴan Nijeriya mazauna arewacin kasar na sayar da katin zaben dindindin (PVCs) kan Naira 2000.

Daraktan Yada Labarai na NEF, Hakeem Baba Ahmed, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin Laraba.

Sanarwar ta ce NEF ta tabbatar da abin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce game da lamarin.

Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne INEC ta bayyana cewa ta bankado yadda wasu ‘yan Najeriya ke sayen katin zabe na PVC tare da gargadin cewa za a daure masu aikata wannan laifi a gidan yari.

Sanarwar ta NEF ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa ta’adar ta yadu sosai kuma ana zuwa wajen raunanan mutane ne a wurare da dama na Arewa da wasu sassan ƙasar domin a saye karin zaɓen su.

Ta ce kungiyar ta bi diddigi kan wannan lamari mai cike da damuwa, inda ta shawarci shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki kan illolin da ke tattare da hana dimbin ‘yan kasa ƴancin su.

“NEF ta yi kira ga INEC da ta kara kaimi wajen wayar da kan jama’a game da wannan mummunar barazana ga ‘yancin masu kada kuri’a.

“NEF ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi da su kara zage damtse wajen yaki da munanan barazanar da ka iya hana miliyoyin masu kada kuri’a a Arewa, da sauran ‘yan kasa da dama a wasu sassan kasar nan kada kuri’a.