Home Labarai Ɗan Arewa ba zai yi wa PDP takarar shugabancin ƙasa a 2027 ba — Bode George

Ɗan Arewa ba zai yi wa PDP takarar shugabancin ƙasa a 2027 ba — Bode George

0
Ɗan Arewa ba zai yi wa PDP takarar shugabancin ƙasa a 2027 ba — Bode George

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Bode George ya bayyana cewa dan arewa ba zai yi wa jam’iyyar takarar shugaban kasa a 2027 ba.

Da ya ke jawabi ga manema labarai kan matsalolin da ke faruwa a jam’iyyar, George ya kuma yi gargadin cewa jam’iyyar na iya yin kasadar faduwa a zaben 2027 har a shafe babin ta idan har ba a samu hadin kai a jam’iyyar ba.

Ya bayyana cewa hadin kan jam’iyyar da hada kan dukkan mambobin ta “su ne sinadarai ga dabarun da za a iya cimma nasara a zabenmu na gaba.”

Sai dai ya yi nuni da cewa, tuni wasu sun fara batun tsayar da dan arewa a matsayin ɗan takara a 2027, yana mai cewa sakamakon zai zama bala’i ga jam’iyyar.

“Dan Arewa ba zai zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar mu a 2027 ba, wannan ita ce magana ta gaskiya.

“A baya wasu membobin da ke rajin wannan ajanda sun san wannan gaskiyar, mafi kyau ga hankalinmu. Ya kamata ‘yan PDP su fahimci wannan gaskiyar tun kafin lokaci ya kure dan PDP daga Kudancin kasar nan ya zama dan takararmu kuma mu mara masa baya domin ya kayar da dan takarar APC a zaben 2027.

“Har 2031, babu wanda ya isa ya yi tunanin tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar mu daga Arewa. Ya kamata dattawan jam’iyyarmu na hakika su tashi su fadi gaskiya.”