
Gwamnatin Taraiya ta baiyana cewa ba ita ta kara farashin litar man fetur ba.
A jiya Laraba ne kamfanin mai na ƙasa l, NNPCL ya sanar da ƙarin litar man fetur daga Naira 897 zuwa sama da Naira 1,000 a fadin ƙasar, lamarin da ya haifar da cece-kuce da kuma alla -wadai ga yan kasar.
Sai dai kuma a hirar da ya yi da Daily Trust, Ministan Yaɗa Labarai da Tarbiyyar Al’umma, Mohammed Idris ya ce ba gwamnati ba ce ta kara farashin mai.
A cewar Ministan, NNPCL ne ya kara farashin man duba da yanayin da ɓangaren mai ya samu kan sa a ƙasar.
Mohammed ya kara da cewa ba gwamnati ba ce ta baiwa NNPCL umarnin ƙarin farashin man ba saboda “gwamnati ba ta da ikon kari ko ragin farashin mai bisa ga yarjejeniyar da ke kunshe a sabon kundin dokar mai,”
Ya ce tun da aka cire tallafin mai a watan Mayun 2023, NNPCL ke cika gibin da ake samu don a saukaka farashin, “inda yanzu kuma NNPCL ya ce bashi da halin ci gaba da cike gibin.”