
Ƙarin sama da mutum miliyan 10 ne suka yi rajistar zabe a aikin rajistar da ake ci gaba da yi a yanzu a fadin Najeriya.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman kanta ta Ƙasa, INEC ce ta bayyana haka a ranar Litinin.
Alƙaluman bayanan sun nuna cewa sabbin masu rajistar sun kai 10,487,972, wadanda kuma suka kammala yin rajistar gaba daya sun kai 8,631,696.
Ya zuwa karfe bakwai na safiyar jiya Litinin 27 ga watan Yuni 2022, masu yin rajistar ta intanet sun kai 3,250,449, masu zuwa da kansu domin a yi musu rajistar kuwa, 5,381,247 ne.
BBC Hausa ta rawaito bayanin ya kuma nuna cewa daga cikin sabbin masu neman rajistar 4,292,690 maza ne yayin da 4,339,006 mata ne, masu nakasa kuma 67,171 sai matasa 6,081,456.