Home Labarai A ƙarshe dai, Muaz Magaji ya fito da ga gidan yari

A ƙarshe dai, Muaz Magaji ya fito da ga gidan yari

0
A ƙarshe dai, Muaz Magaji ya fito da ga gidan yari
Bayan ya shafe kwanaki goma sha biyu a gidan yari, a ƙarshe dai Muaz Magaji, babban ɗan adawar Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya shaƙi iskar ƴanci.
Kotun Majistare mai lamba 58 da ke zaman ta a unguwar Nomansland ce dai ta aike da shi gidan yarin tun 31 ga watan Janairu.
Kotun Majistare ɗin, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aminu Gabari ce ta bada belin Magaji, wanda a ka fi sani da Ɗan-Sarauniya, bayan ta aike da shi gidan yari tun a ranar 31 ga watan Janairu.
Kotun dai na tuhumar Magaji da laifuka huɗu da su ka haɗa da ɓata suna, cin mutunci da gangan, ƙarya da nufin zubar da kima da kuma ta da hankali, laifukan da su ka saɓa da sashe na 392, 399 da 114 na kundin dokar Kano ta 1999, amma kuma ya musanta duka laifukan.
Ƙa’idojin belin da kotun ta bayar da farko sun haɗa da naira miliyan 1 da kuma waɗanda za su tsaya masa mutum biyu.
A cikin mutum biyun da za su tsaya masa, in ji alƙalin, a kwai Dagacin ƙauyen Ɗan-Sarauniya, sai kuma Kwamnadan Hisbah na Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ko kuma Babban Limamin Ƙaramar Hukumar.
Hakazalika kotun ta bukaci Magaji da ya kai mata fasfo ɗin shi na tafiye-tafiye, inda su ma mutum biyun da za su tsaya masa sai sun kai hotunan su.
Sannan kotun za ta tura ma’aikatan ta su duba gidajen mutum biyun da za su tsayawa Magaji.
Sai dai kuma Magaji bai iya cika waɗannan ƙa’idoji ba sakamakon babban limamin Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa bai je ya wakilci shi ba.
Ganin haka ne sai sai lauyan Magaji, Ghazzali Ahmad, ya miƙawa alƙalin kotun roƙon su na a sassauta sharuɗɗan belin.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a zaman kotun na jiya Juma’a, alƙali Gabari ya karɓi rokon sassauta belin, inda ya umarci a kawo babban limamin ƙauyen su Magaji ɗin, wato ƙauyen Ɗan-Sarauniya, a maimakon na Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa.
Kotun ta kuma umarci Magaji da ya biya gilashin motar Gidan Yari da a ka faɗa lokacin da a dauko shi za a kawo shi kotun.
A yau Asabar ne dai, ƴan awanni kaɗan da su ka gabata, Magaji ya cika sharuɗɗan belin, inda tuni a ka fito da shi da ga gidan yari.
Sai kuma watan Maris za a ci gaba da shari’ar.