Home Labarai Ƙaruwar sakin aure a Nijeriya abin damuwa ne — Malami

Ƙaruwar sakin aure a Nijeriya abin damuwa ne — Malami

0
Ƙaruwar sakin aure a Nijeriya abin damuwa ne — Malami

Wani limamin fasto mai suna Fasto Ayobami Moses na cocin Christ Dominion dake Ilorin ya bayyana damuwarsa kan ƙaruwar sakin aure tsakanin ma’aurata a kasar.

Moses, wanda ya bayyana damuwarsa a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Ilorin a ranar Juma’a, ya ce yawan rabuwar aure a tsakanin ma’aurata a zamanin nan ya zama abin ban tsoro.

A cewarsa, yanzu haka ma’auratan matasa sun dauki saki a matsayin mafita mafi kyau ga duk wani karamin rashin jituwa tsakanin su.

Moses ya bukaci ma’aurata su koyi gyara al’amura ta hanyar tattaunawa da kuma juriya maimakon neman rabuwar aure.

“Su daina garzayawa kotu domin a raba aurensu. Babu wani aure da yake da dadi ɗari bisa ɗari,” inji shi.

Malamin ya ce galibi, dalilan suke haifar da sakin aure basu taka kara sun karya ba.

Ya ce za a iya sasanta ‘yar rashin fahimta ta hanyar sulhu a tsakanin ma’aurata domin a ceto aurensu.

Musa ya shawarci ma’aurata su ƙoƙarta su yi karanci halayen abokan zamansu sosai don ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninsu.