
Ireland na shirin ƙara mafi ƙarancin shekarun fara shan sigari zuwa 21, bisa ga tsarin da majalisar ministoci ta amince da shi.
A cikin wata sanarwa da majalisar ministocin ta fitar a jiya Talata ta ce tsarin zai sa Ireland ta zama kasa ta farko a Tarayyar Turai da ta dauki irin wannan matakin.
Ya ce matakin ya zo ne shekaru 20 bayan Ireland ta zama kasa ta farko a duniya da ta hana shan taba a wuraren aiki da na al’umma suka hada da mashaya da gidajen abinci.
A halin yanzu, kashi 18 cikin 100 na mutanen da suka haura shekaru 15 suna shan taba sigari a ƙasar.
An ɓullo da sabuwar dokar ne don rage yawan shan taba a Ireland zuwa kasa da kashi biyar cikin dari.
Shan taba na kashe kimanin mutane 4,500 a duk shekara a Ireland.
Ministan Lafiya Stephen Donnelly ya ce matakin “na tsauri” ne, ya kara da cewa ” illolin shan taba sigari na da yawa kuma yana bukatar mataki mai tsauri.”