
Allah Ya yi wa mutumin da ya shafe shekara 70 yana sallah a bayan limaman Masallacin Ka’aba Sheikh Muhammad bin Abdul-Wahhab Aal Ash-Sheikh rasuwa.
Sheikh Muhammad ya rasu ne a yau Laraba, 25 ga watan Mayu wanda ya yi daidai da 24 ga watan Shawwal a wani asibiti a birnin Jiidah na Saudiyya.
YAna daga cikin mutanen da suka samu albarkar yin sallah a bayan limaman Masallacin Harami, kuma ya shafe shekara 70 yana yin hakan.
Ana yawan ganinsa a bidiyo a bayan limaman a cikin shekara 10 da suka wuce.