Home Labarai Ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Bello Turji ya saki mutane 52 da yai garkuwa da su

Ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Bello Turji ya saki mutane 52 da yai garkuwa da su

0
Ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Bello Turji ya saki mutane 52 da yai garkuwa da su

 

Ƙasurgumin jagoran ƴan fashin dajin nan Bello Turji ya saki mutane 52 da yai garkuwa da su a Jihar Zamfara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Wani mazaunin jihar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya baiyana cewa an ɗauki mutanen da a ka saki da ga jeji zuwa inda a ka yi alkawari da Turji za a haɗu a ɗauke su zuwa garin Shinkafi.
“An jera motocin kiya-kiya kuma a ka basu umarnin su je Maberiya, wani gari kusa da Shinkafi,” in ji mazaunin.
Shi Turji shine ke shirya duk kashe-kashe da garkuwa da mutane da a ke yi a yankin Ƙananan Hukumomin Shinkafi, Sabon Birni da Isah a Zamfara da Jihar Sakkwato.
A tuna cewa a watan Disamba da ya gabata ne rahotanni su ka baiyana cewa Turji ya rubuta wasiƙa zuwa masarautar Shinkafi, inda ya nuna aniyar sa ta ajiye makamai da rungumar zaman lafiya.
Wasu majiyoyi sun baiyana cewa sakin mutane 52 ɗin wani ɓangare ne na tattaunawa da a ke yi da Turji.