Home Ilimi ASUU ta ƙara makonni 8 a kan yajin aikin da ta ke yi

ASUU ta ƙara makonni 8 a kan yajin aikin da ta ke yi

0
ASUU ta ƙara makonni 8 a kan yajin aikin da ta ke yi

 

Yayin da a yau wa’adin yaƙin aikin gargaɗi na wata ɗaya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta ke yi, ƙungiyar ta kuma sanar da tsawaita yajin aikin da da makonni 8 sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnati kan bukatunsu.

ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da jarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na kasar.

Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau jami’i ne a kungiyar ta ASUU, ya ce sun dauki matakin kara wa’adin ne domin bai wa gwamnati damar cimma sahihiyar matsaya, ta yadda ba sai sun kara tafiya wani yajin aikin nan gaba ba.

Ya ce makonni 8 sun wadatar matukar gwamnatin da gake ta ke kan daukar matakin da ya dace.

ASUU dai na ganin yajin aikin ne hanyar karshe da take bi domin tilasta wa gwamnatin Najeriya biya mata bukatunta.

Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda.

Yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.

Wasu bayanai sun nuna cewa kungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.