Home Labarai ASUU ta ƙara makonni 4 a kan yajin aikin da ta ke yi

ASUU ta ƙara makonni 4 a kan yajin aikin da ta ke yi

0
ASUU ta ƙara makonni 4 a kan yajin aikin da ta ke yi

 

 

 

Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta sanar da tsawaita yajin aikin da take yi da makonni hudu.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Litinin, mai ɗauke da sa hannun shugabanta na kasa, Emmanuel Osodeke, a karshen wani taron gaggawa da ta yi a jiya Lahadi a Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa; “Bayan tattaunawa mai zurfi tare da fahimtar gazawar gwamnati a baya wajen bin ka’idojinta na magance matsalolin da suka taso a cikin yarjejeniyar FGN/ASUU ta shekarar 2020 (MOA), NEC ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin da makonni huɗu, domin baiwa gwamnati karin lokaci na ta warware dukkanin matsalolin .

A cewar Osodeke, yajin aikin zai fara aiki ne daga karfe 12.01 na safe na ranar Litinin, 1 ga Agusta, 2022.