
Ƙungiyar malaman jami’oi a Nijeriya, ASUU ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin da take gudanarwa da ƙarin watanni 6.
Jaridar Punch ta rawaito cewa matakin ya zo ne bayan wata zazzafar tattaunawa da aka yi a yau Litinin game da yadda za a cimma matsaya tsakanin ƙungiyar da kuma gwamnati.
An ɗauki matakin ci gaba da yajin aikin bayan ganawar kwamitin zartarwa a hedikwatar ASUU da ke Jami’ar Abuja, babban birnin Najeriya.
Ƙungiyar ASUU dai ta shafe watanni tana gudanar da yajin aikin da ya tilastawa ɗaliban jami’oin gwamnati zama a gida.
ASUU na ganin gudanar da yajin aikin ne hanyar samun mafita ga tarin buƙatun da ta gabatar wa gwamnatin Najeriya ciki har da batun inganta musu albashi.