
Yau shugabannin kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ke gudanar da taro a Abuja domin yanke hukunci akan makomar yajin aikin da suke yi wanda ya zarce watanni 6 yanzu haka.
Rahotanni sun ce taron ya biyo bayan irin sa da jami’o’in kasar sama da 100 suka gudanar domin bayyana matsayin su akan yajin aikin da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.
Ministan ilimin Najeriya, Adamu Adamu ya shaidawa manema labarai cewar sun cimma yarjejeniya guda 4 daga cikin batutuwa 5 da malaman suka gabatar, banda batun biyan albashin watanni 6 da su ka kwashe su na yajin aiki, wanda gwamnati ta ce ba za ta biya malaman ba saboda ba su yi aiki ba tsawon watannin.
Sai dai malaman sun ce babu gaskiya akan matsayin da gwamnati ta shaidawa jama’a, domin kuwa har yanzu gwamnati bata amince da bukatun da suka gabatar na inganta makarantun da kuma samar musu da kayan aikin da ake bukata domin bada ilimi ba.
Rahotanni sun ce jami’o’I sama da 100 sun bayyana goyan bayan zarcewa da yajin aikin na ‘illa ma-sha-Allahu’, matakin da ake sa ran taron shugabannin na yau ya tabbatar.
Wannan matsala ta yajin aikin ya taimaka gaya wajen katse duk wani harkokin bada ilimi a manyan makarantun na gwamnati da kuma ayyukan binciken da ake gudanarwa.
Iyayen ɗalibai a kasar na ci gaba da bayyana matukar damuwar su akan yadda aka gaza warware matsalar wadda ke barazana ga aikin samar da ilimi da kuma makomar ƴaƴansu.