
Wasu masu ruwa da tsaki sun nuna damuwarsu kan matakin da gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU za su iya ɗauka na sasanta wa a yayin da wasu jami’o’in jihohi ke fice wa daga yajin aikin.
Masu ruwa da tsakin sun bayyana damuwar su ne a wata tattaunawa daban-daban da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja a yau Talata.
Jami’o’in jihohin da suka fice daga yajin aikin na iya fuskantar barazanar rasa wasu tagomashi daga Gwamnatin Tarayya da ASUU.
Farfesa Stephen Onah, tsohon Babban Darakta na Cibiyar Lissafi ta kasa ya ce gwagwarmayar ASUU ta kasance ga jami’o’in gwamnati waɗanda jami’o’in jihohi ke cikin su.
“Idan Jami’o’in Jihohi suka fice daga karshe Gwamnatin Tarayya za ta iya janye tallafin Manyan Makarantu (TETfund) wajen tallafa musu.
“Ilimi yana cikin jerin ikon gwamnatin tarayya da ts jihohi, kuma ita ASUU a matsayin ta na kungiya, da dage cewa dole a jami’o’in jihohi na TETfund a farkon farawa.
“Jami’o’in Jihohi za su yi asara fiye da ASUU a matsayin kungiya. Yawancin Gwamnonin Jihohi sun san wannan gaskiyar.
“Babu shakka ASUU za ta fuskanci koma baya na wucin gadi,” in ji Mista Onah.