
Kungiyar malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU ta ce wa’adin makonni biyun da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar domin warware matsalolin da kungiyar ta gabatar ya yi yawa.
Ga malaman jami’o’i, ba zasu haura fiye da kwanaki biyu ba tare da sun magance matsalolin da suka jefa tsarin jami’o’in gwamnati na kasar cikin yajin aikin da ya tsawaita har zuwa watanni biyar ba.
Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana hakan ta cikin shirin gidan Talabijin na Channels mai suna Siyasa a yau” a jiya Talata a Abuja.
“Makonni biyu sun yi tsayi sosai,” in ji shi.
“Batun sake tattaunawa an kammala shi daga bangarorin biyu. abinda muke jira daga kareku shi ne ku dawo ku ce mana ‘kun amince’, hakan ba zai dauki kwana biyu ba. An bayyana mana cewa sun kashe biliyoyin kudi don ciyar da yara a makaranta; shin haka ne, yara nawa kuka ga ana ciyar da su?
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a jiya Talata ne dai Shugaban kasa ya gana da Ministan Ilimi, Adamu Adamu, da Kuma wasu cikin ministocinsa dake da ruwa da tsaki cikin lamarin, inda ya samu bayanai kan yadda ake takun saka tsakanin gwamnati da kungiyoyin jami’o’i ciki har da ASUU.
A wajen taron, Buhari, ya umarci ministan ilimi da ya samar da mafita kan yajin aikin da malaman jami’ar ke ci gaba da yi tare da kawo masa rahoto nan da makonni biyu.