
Ɗan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce muddin ya zama shugaban kasa, kungiyar malaman jami’a ta ASUU ba za ta sake shiga yajin aiki ba.
Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin magana a bikin ranar matasa ta duniya a Abuja yau Juma’a, inda ya ce mahaifinsa bai so yaje makaranta ba, amma daga baya ya jajirce da kuma shiga makaranta har zuwa matakin jami’a.
Wazirin na Adamawa ya kara da cewa hakkin kowani matashi shi ne samun ilimi, inda ya ce yajin aiki da kungiyar malaman jami’a ta ASUU ke yi da kuma rashin magance matsalar su da gwamnati ta gaza yi da cewa abin damuwa ne.
Ya kara da cewa hakan ba za ta taba faruwa ba a karkashin gwamnatin PDP ko kuma gwamnatinsa idan aka zabe shi.
Har ila yau, Atiku ya ce shi mutum ne mai bunkasa harkokin ilimi, inda ya kuma ce hakkin kowace gwamnati ne ta tabbatar an bai wa kowani matashi a kasar hakkokinsa musamman a bangaren ilimi.