Home Labarai Ɓatagari sun ƙona gidaje 10 bisa zargin sace musu babur a Kano

Ɓatagari sun ƙona gidaje 10 bisa zargin sace musu babur a Kano

0
Ɓatagari sun ƙona gidaje 10 bisa zargin sace musu babur a Kano

 

Wasu ɓatagari sun kai hari kan garin Dan Jamfari da ke kauyen Barbaji a Ƙaramar Hukumar Rogo a jihar Kano, tare da ƙona gidaje 10.

Babban Sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, Saleh Jili, a jiya Juma’a ya ce hukumar ta jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da kai musu kayan agaji.

Ya ce gwamnatin jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai ta kamo wadanda suka kai harin domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Kayayyakin agaji da aka baiwa wadanda abin ya shafa sun haɗa da bandir na kwanon rufi guda 10, buhunan siminti 20, fakiti 10 na kusoshi na zinc, buhunan shinkafa mai nauyin kilo 10 guda 20, masara 20 da gishiri buhu biyar.

Wadanda abin ya shafa sun kuma samu kayan sawa, bokitai, man gyada da kwali guda biyar na kayan dandano.

Jili ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, sannan ya bukaci mazauna yankin da su zauna lafiya da juna.

Wani mazaunin garin, Magaji Audu ya bayyana cewa maharan na dauke da sanduna da adduna su ka shigo garin.

“su sama da 200 su ka mamaye kauyen cikin dare suna bi gida-gida suna neman babur dinsu da su ka ce an sace.

“Maharan sun yi kokarin caka mani wuka a gaban iyali na, ni kuma na ki fito da ‘ya’yana wadanda suka ce sun sace babur kamar yadda suka bukata,” inji shi.

Audu ya ƙara da cewa, washegari sai matasan su ka dawo, inda su ka sanya wa gida na wuta da sauran gidaje, inda da kyar ni da iyali na mu ka sha.