Home Siyasa Atiku Abubakar ba shi da wata alkibla tunda ya sake komawa PDP – Masari

Atiku Abubakar ba shi da wata alkibla tunda ya sake komawa PDP – Masari

0
Atiku Abubakar ba shi da wata alkibla tunda ya sake komawa PDP – Masari
Gwamnan jihar Katsina AMinu Bello Masari

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana komawar tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar jam’iyyar PDP a matsayn wata gazawa da kuma rashin alkibla a siyasance.

Masari ya bayyana haka ne, ranar litinin a garin MaiAduwa. Haka kuma, ya bayyana cewar komawar Atiku PDP ko kadan ba zata shafi nasarar da APC zata samu anan gaba ba, yace daman Atiku fa shi kadai yake zikau ba shi da kowa.

Jam’iyyar APC ita ce mafitar ‘yan Najeriya, domin tana yin dukkan abinda zata iya domin magance matsalolin da suka dabaibaye kasarnan, haka kuma yace, APC ta baiwa matasa dama sosai a Gwamnatinta, inda suka samu kashi 65 da muakamai.

Masari ya kara da cewar siyasar ko a mutu ko ai rai ta gushe a Najeriya. A yanzu kowane dan siyasa halinsa ne zai bishi, babu wani ci da buguzum da za aiwa ‘yan Najeriya.

Yace APC na samun nasarori a jihohi da kuma Gwamnatin tarayya, yace zuwa Shekara mai zuwa APC zata karbi manyan mutane da zasu baro jam’iyyunsu su dawo APC, domin sun ga cewar ita ce mafita.

Gwamna Aminu Bello Masari yana MaiAdua ne domin karbar tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Yau Gwajo Gwajo, wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.