
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya amince da naɗin Dakta Ali Bappayo Adamu a matsayin mataimakinsa na musamman kan harkokin kasuwanci a shiyyar Arewa-maso-Gabas.
Atiku ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai dauke da sa hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe a yau Litinin.
Bappayo, wanda nadin nasa ya fara aiki nan take, kamar yadda sanarwar ta bayyana, matashin dan Najeriya ne mai kishin kasa.
Sanarwar ta bayyana Bappayo a matsayin, “mutum ne mai kishi, wanda manufarsa ita ce bayar da gudunmawa wajen inganta rayuwar marasa galihu a cikin al’umma.”
“An haifi Ali Bappayo Adamu a garin Gombe a ranar 19 ga Maris, 1986. Ya yi karatun digiri a kan fannin Ilimin Kiwon Lafiya daga Jami’ar Maiduguri, Digiri na biyu a fannin Kiwon Lafiyar Jama’a daga Jami’ar Bayero da Digiri a fannin Kiwon Lafiyar Jama’a daga Jami’ar Taxila American University.
“Bappayo ya kasance ma’aikacin ƙwarewa na musamman Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da kuma wanda ya kafa Kasuwancin Arewa-maso-Gabas na Atiku 2023,” in ji sanarwar.