Home Labarai 2027: Atiku, Kwankwaso da Obi na tattaunawar yin maja – PDP

2027: Atiku, Kwankwaso da Obi na tattaunawar yin maja – PDP

0
2027: Atiku, Kwankwaso da Obi na tattaunawar yin maja – PDP

Manyan ƴan jam’iyyun adawa uku a Nijeriya na tattauna yiwuwar yin maja domin karbe mulki daga hannun APC a zaben 2027.

Mataimakin mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Ibrahim Abdullahi ne ya yi bayanin hakan a shirin gidan Talabijin na Channels.

Channels ta rawito shi ya na cewa manyan ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP da Sanata Rabi’u Kwankwaso na NNPP za su ajiye banbancen dake tsakaninsu wajen hadewa guda don tunkarar APC a 2027.

Abdullahi, ya ce da ace jam’iyyar ta PDP ta yi maganin rikicin dake cikinta a daidai lokacin da Wike da Kwankwaso da Obi ke cikin jam’iyyar da sai sun kayar da Tinubu da APC a zaben 2027.

Ya ce, “Mun rasa Kwankwaso, kuma mun rasa Peter Obi, dukkan wadannan mutane, kayi tunani idan da ace suna jam’iyyar da mun lashe zabe.

” Su APC sun kada mu zabe da kuri’u miliyan 1 da wani abu. Dan takara daya na wadanda na ambata zai iya maye gurbin kuri’un da kafa muna kan karagar mulki a yau”.