
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya nada Dino Melaye da Dakta Daniel Bwala a matsayin masu magana da yawunsa a yakin neman zaɓen shugaban kasa a 2023.
Abubakar a wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar a Abuja a yau Alhamis, ya ce naɗin ya fara aiki nan take.
Melaye, wanda ya fito daga Ayetoro Gbede a Ƙaramar Hukumar Ijumu a Kogi, dan majalisar dattawa ta 8 ne, wanda ya wakilci Kogi ta Yamma a majalisar dokokin kasar.
Shi kuma Bwala, wanda ya fito daga Adamawa, ya kasance kwararre a fannin shari’a kuma manazarci kan harkokin jama’a, kafin nadin nasa.