Home Siyasa Atiku ya bada tallafin Naira miliyan 30 ga ƴan PDP da su ka yi haɗari a Plateau

Atiku ya bada tallafin Naira miliyan 30 ga ƴan PDP da su ka yi haɗari a Plateau

0
Atiku ya bada tallafin Naira miliyan 30 ga ƴan PDP da su ka yi haɗari a Plateau

A jiya Lahadi ne dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ziyarci jihar Plateau kan hadarin da ya yi sanadin mutuwar magoya bayan jam’iyyar 16 tare da jikkata wasu 83.

Motar da ke jigilar magoya bayan jam’iyyar, galibi yara maza ne daga taron jam’iyyar na shiyyar a karamar hukumar Pankshin ta jihar, ta yi hatsari a kusa da wata gada a unguwar Panyam, Ƙaramar Hukumar Mangu ta jihar.

Atiku ya sanar da bayar da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci jihar tare da shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu da wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya kuma kai ziyarar ta’aziyya ga tsohon gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang, a gidansa na Du kasa dake Jos.

Atiku ya yabawa Jang bisa jagorancin jam’iyyar PDP a Plateau, ya kuma ba shi tabbacin cewa, “Babu wanda ya yi sadaukarwa ba tare da an yaba da sadaukarwar ba.”

Shima da ya ke jawabi, Ayu ya kuma jajanta wa ƴan jam’iyyar PDP na jihar da kuma al’ummar jihar baki daya kan wannan lamari mai ban tausayi, ya kuma yi addu’ar Allah ya ba su ikon jure rashin da ba za a iya kwatantawa ba.

MAyu ya kuma sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 10 ga wadanda hatsarin ya rutsa da su a madadin jam’iyyar PDP ta kasa kuma ya ce sadaukarwar da suka yi ba za ta kasance a banza ba.

Ya ba da tabbacin cewa za su ci gaba da yin aiki tukuru ba wai kawai ga PDP ba, har ma da kasar “domin sake gina kasar da manyan kayan aiki wanda hakan ba zai sake faruwa ba.”