Home Labarai Atiku ne kaɗai zai iya gyara barnar APC idan aka zaɓe shi a 2027– Suwaid

Atiku ne kaɗai zai iya gyara barnar APC idan aka zaɓe shi a 2027– Suwaid

0
Atiku ne kaɗai zai iya gyara barnar APC idan aka zaɓe shi a 2027– Suwaid

Jagoran Kungiyar PDP Jirgin Fiton Al’umma, Bashir Suwaid ya baiyana cewa dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar me kadai zai iya gyara barnar da gwamnatin APC ta yi a shekarar ta tara tana mulkin Nijeriya.

A wata sanarwa da ya sanyawa hannu a yau Asabar a Kano, Suwaid ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya damu da halin kunci da talakawan Nijeriya su ka tsinci kansu a hannun APC.

A cewar sa, yayin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta jefa yan Nijeriya cikin mawuyacin hali sakamakon manufofinta masu tsauri, shi kuma Atiku na ta kokarin tsara yadda zai samar wa talaka sauki idan ya samu mulkin kasar a 2027.

Bashir Suwaid tare da Atiku Abubakar 

“Ko a kwanan nan ma da Bode George ke cewa ba za a baiwa Atiku takara a 2027 ba, Kakakin shi Atiku din, Paul Ibe ya fito ya ce mai gidan sa ba 2027 ce a ran shi ba, shi tunanin yadda talaka Nijeriya zai fita daga halin kuncin da ake ciki ya ke.

“yayin da Nijeriya ta lalace ta kowanne bangare, Atiku Abubakar, wanda shugaba ne da bashi da son rai da bangaranci, shi kadai ya rage mana a kasar nan da zai gyara duk wasu kura-kurai tare da dora Nijeriya kan gwadaben ci gaba da haɓakar arziki.

“yayin da barnar APC ta shekara 9 ta sanya ƴan Nijeriya su ka fitar da rai na gyara a ƙasar nan, kwarewa da sanin makamar aiki irin na Atiku shi ya sanya ya zama jirgin fiton al’umma a zaben 2027.

“Saboda haka ina kira ga ƴan Nijeriya da su fito ƙwansu da kwarkwatarsu su zabi Atiku a 2027 domin gyaran Nijeriya,” in ji Suwaid.