
A ranar Laraba ne dai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar zai sanar da takarar shi ta shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa na 2023.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Atiku zai sanar da takarar ta shi ne bayan ya ɗauki watanni ya na tuntubar masu ruwa da tsaki a ciki da wajen ƙasar nan.
A wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran Atiku ya fitar a Abuja, za a yi taron ne a International Conference Centre da misalin ƙarfe 11 na safe, inda a ke tsammanin ƴan ‘uwa, abokan gwagwarmaya, jagororin siyasa, ƴan jam’iya da kuma magoya bayan Atiku za su halarta.
Sanarwar ta ce taron shine aza tubalin shiga yaƙin neman zaɓen Atiku ɗin a ƙarƙashin jam’iyar adawa ta PDP.
A makon da ya gabata ne dai Atiku ya baiyana cewa wata kungiyar ƴan kasuwa ta Arewa ta sai masa fom ɗin takara.