
Rundunar Ƴan Sanda ta Ƙasa a Jihar Kaduna ta tabbatar da kwance da wani bam a wata mashaya a ranar 27 ga Febrairu, rana ɗaya da wani bam ya tashi a otal a jihar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Mohammed Jalige ya fitar a jiya Talata, an kwance ban ɗin ne a mashaya mai suna Larry Breeze Bar da ke unguwar Rotimi a Ƙaramar Hukumar Chikun.
A cewar sa, bayan ban ɗin da ya tashi a otal, sai rundunar ta samu rahoton ganin wani a cikin leda a mashayar, inda magoya bayan ƙwallon ƙafa ke kallon wasa.
Ya ce rundunar, da ga jin ƙarfin rahoton, nan da nan ta tura rundunar ta masu ƙwarewar kwance bam, inda a ka kewaye yankin kuma a ka kwance bam ɗin lami-lafiya.
Jalage ya ƙara da cewa fashewar bam ɗin farko ta faru ne a otal ɗin Dorino da ke Kabala ta Kudu a cikin birnin Kaduna.
Ya ce gurin kaɗan fashewar bam ɗin ta lalata, inda ya ƙara da cewa ba a yi asarar rai ba.
Kakakin ya ce Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar ya hori al’umma da su kai rahoton wani motsi ko wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa caji-ofis mafi kusa, inda ya yi kira da kowa ya ci gaba da harkokin yayin da ƴan sanda ke ci gaba da kokarin kare rayuka da duniyoyi.