Home Siyasa Ku ƙauracewa zaɓen fidda shugabanni na mazaɓa, ɓangaren Yari ya shawarci ƴan APC a Zamfara

Ku ƙauracewa zaɓen fidda shugabanni na mazaɓa, ɓangaren Yari ya shawarci ƴan APC a Zamfara

0
Ku ƙauracewa zaɓen fidda shugabanni na mazaɓa, ɓangaren Yari ya shawarci ƴan APC a Zamfara

 

Lawal Liman, Shugaban Riƙo na Jam’iyar APC a Jihar Zamfara, ɓangaren tsohon gwamnan jihar, Abdul’aziz Yari ya yi kira ga mabiya tsagin nasu cewa kada su shiga zaɓen shugabannin jam’iya na mazaɓa wanda ɓangaren gwamna mai ci, Bello Matawalle ya gudanar a ranar Asabar, 13 ga watan Nuwamba.

Wannan kiran na ƙunshe ne a wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na ɓangaren, Ibrahim Birnin-Magaji ya fitar a yau Asabar a Gusau.

“Kun san cewa akwai umarnin da kotu ta bayar na a dakatar da duk wani zaɓen shugabannin jam’iya har sai abinda kotun ta yanke a bisa rushe shugabannin jam’iya na jiha daga uwar jam’iyar APC ta ƙasa.

“A kan hakane, jagoran mu, Alhaji Abdul’aziz Yari ya umar ƴan jam’iyar APC a jihar nan, a ƙarƙashin shugabancin Lawal Liman da mu ƙauracewa zaɓukan shugabannin jam’iya tun daga na mazaɓa, ƙanan hukumomi da na jiha wanda gwamna Bello Matawalle ya shirya a yau Asabar, 13b ga watan Nuwamba.

“Sabo da haka ina kira da mu ƙara haƙuri mu kuma zama masu bin doka, sannan mu jira umarnin da za a bayar nan gaba,” in ji shi.