Home Ƙasashen waje Ƴan awaren Ukraine sun yi nasara a zaɓen haɗewa da Russia

Ƴan awaren Ukraine sun yi nasara a zaɓen haɗewa da Russia

0
Ƴan awaren Ukraine sun yi nasara a zaɓen haɗewa da Russia
Mahukuntan yankunan ‘yan awaren Ukraine da ke karkashin ikon Rasha, sun yi ikirarin samun nasara a zaben raba gardamar ballewa daga kasar, abin da ya janyo cece-kuce daga kasashen yammacin Turai. Matakin da ke zuwa a dai dai lokacin da Moscow ta yi gargadin cewa za ta iya amfani da makaman nukiliya don kare yankunan da a yanzu suka koma na ta.
Tuni dai Ukraine da kawayenta suka yi tir da zaben na raba gardama, wanda suka bayyana shi a matsayin shirme, suna masu cewa kasashen yammacin duniya ba za su taba amincewa da sakamakon kuri’un da aka kada ba, wanda ko shakkah babu ya kara girman tasirin mamayar da Rasha ta yi wa kasar ta Ukraine na tsawon watanni bakwai.
A Zaporizhzhia, mahukuntan ‘yan awaren Ukraine sun ce kashi 93.11 cikin 100 na masu kada kuri’a sun goyi bayan komawa karkashin Rasha, yayin zaben raba gardamar da aka kammala a jiya Talata.
A Kherson, yankin da Rasha ta mamaye a kudancin Ukraine, jami’ai sun ce sama da kashi 87 na masu zabe sun goyi bayan komawa hannun Moscow.
A Lugansk da ke Gabashin Ukraine da ke karkashin ikon ‘yan aware, mahukuntan yankin sun ce sama da kashi 98.42 cikin dari ne suka kada kuri’ar amincewa komawa karkashin Rasha.
Yanki na karshe da zaben raba gardamar neman ballewa daga Ukraine ya gudana shi ne, Donetsk inda a nan ma hukumar zabe ta ce kashi 99.23 na kuri’un da aka kada na goyon bayan hadewa da Rasha ne.