Home Siyasa Alƙawari na ɗauka cewa zan hidimta wa ƴan Nijeriya — Buhari

Alƙawari na ɗauka cewa zan hidimta wa ƴan Nijeriya — Buhari

0
Alƙawari na ɗauka cewa zan hidimta wa ƴan Nijeriya — Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Litinin ya ce ya alkawari ya ɗauka cewa zai yi wa Najeriya da ‘yan Najeriya hidima gwargwadon ikonsa.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wa mai martaba Sarkin Bauchi, Rilwanu Adamu ziyara a yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a Bauchi.

“A shekarar 2003 da 2012 na ziyarci daukacin kananan hukumomin kasar nan guda 774, kuma a shekarar 2019 da na sake tsayawa takara karo na biyu na ziyarci dukkan jihohin kasar nan.

“Don haka, a can na yi alkawari da alkawarin cewa zan bauta wa Najeriya da ‘yan Nijeriya iyakar iyawa ta,” inji shi.

Shugaban wanda ya kuma yabawa Sarkin bisa kyakkyawar tarba da aka yi masa, ya yabawa Gwamna Bala Mohammed kan yadda ya ke gudanar da ayyuka masu inganci a jihar.

A nasa jawabin, Adamu ya gode wa shugaban kasa bisa wannan ziyara, sannan ya bukaci ‘yan siyasa da su rika yin siyasa ba tare da cin mutuncin juna ba.