Home Labarai Ɗaya daga cikin malaman da su ka jagoranci muƙabalar Abduljabbar ya rasu

Ɗaya daga cikin malaman da su ka jagoranci muƙabalar Abduljabbar ya rasu

0
Ɗaya daga cikin malaman da su ka jagoranci muƙabalar Abduljabbar ya rasu

 

 

 

Malam Mas’ud Mas’ud Hotoro, ɗaya da ga cikin malaman da su ka jagoranci mukabala da malam Abduljabbar Nasiru Kabara ya rasu.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa Malam Mas’ud ya rasu ne a daren jiya Laraba, sakamakon haɗarin mota a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Idan za a iya tunawa malamin na cikin malamai huɗu da su ka yi Muƙabala da Abduljabbar a kwanakin baya.

Malamin shi ne wanda ya wakilci ɓangaren Ƙadiriyya ya yin zaman muƙabalar.

Rahotanni sun baiyana cewa za a yi jana’aizar malamin a yau Alhamis a gidansa da ke Hotoro da karfe 2:00 na rana.