
Akwai abubuwan da zai yi wahala ka fahimce su, ko ka gane haƙiƙanin yadda suke in ba samunka su ka yi ba, ko wajen samun su ka zo ba. Wata rana wani dattijo yake mana gargadi game da sharrin hassada da mahassada.
Bayan mun bar wajen sa sai abokina yake cewa kaji fa mutumin da ko 1M bai da ita a account shine ke magana akan mahassada, to ayi hassada akan me kenan? Sai nace masa abin da ya fada gaskiya ne komai ƙanƙantar baiwa ko ni’imar da Allah yayi ma sai kaga wani wannan ni’imar ke tada masa hankali da hanashi bacci. Kaga dole a nemi tsarin Allah a kuma yi taka tsantsan.
Duk da haka abokina bai gamsu ba. Watanni uku baya ya kirani yana min koken yadda wasu mahassada suka sako shi gaba da sharri da ƙulle-ƙulle. Niko na tuntsure da dariya nace abokina ko ka zama millionaire ne shi yasa aka fara maka hassada? Tuni na tuna masa gargadin da dattijon nan ya mana, ai ko yace yallaboi gaskiya ya fada.
Kwanan baya wani mutum mai aikin casual (na shara) a asibiti yake bani labarin yadda wani abokin aikin sa dan casual ya tsani ganin sa kamar ya jefa shi a wuta, sabo da kawai Allah ya masa baiwar jama’a kowa na son mu’amala da shi da kuma ɗan ihsanin da ma’aikata ke masa Jifa-jifa. Yace lamarin har ya kai ga idan mahassadin ya ganshi take idanun sa ke canja launi zuwa ja-jazur, saboda baƙar ƙiyayya da hassada.
Ka zama mu’umini mai cikakken imani da ƙaddara mai kyau da akasinta. Shi Allah cikin lamurran Sa baya shawara da kowa wajen sarrafa ƙaddara, baiwa, ɗaukaka, arziki, falala, talauci, jinya, ƙasƙanci, fitina ko lafiyar bayin Sa. Mabuwayi ya tsarkaka ya kadaita wajen raba arzikin bayin Sa, wanda ya samu arziki, baiwa, ni’ima, daukaka ko falala haka Allah yaso ba don yafi kowa ba, ko yafi kowa can-canta ba hassalima tausayi ne irin nasa Mabuwayi da kuma jarrabawa.
Wanda ko Allah ya ƙaddarama talauci, jinya, rashi da koma bayan rayuwa shima ba don Allah baya son sa bane, ko yayi ma Allah laifi ba, hasalima adalci ne irin naSA Mabuwayi da kuma jarrabawa. Ɗan uwa kada ka bari ka samu matsala a sha’anin imani da ƙaddara.
Sai ka ƙare tunani wai takameme mai ya haɗaka da wane ka rasa dalili na zahiri. Dalilin kuwa a bayyane yake wata falala, ko baiwa ko ni’ima da Allah yama ne baya son ka da ita. Ba lalle sai ka zama mai kuɗi ko mai mulki ko wani shahararre za’a ma hassada ba, kai wasu hatta shiriya ka zama cikakken mutum baka shaye-shaye, baka bin mata ko aiki ash-sha, baka neman jafa’i ka kimtsu ka zama nagari saboda wannan kadai sai kaga wani nama hassadar zama mutumin ƙwarai.
Allah Sarki! Yayin da kake ganin Allah yayi ma waninka ni’ima bubba idan ka duba a tsanake zaka ga kaima Allah yama wata ni’imar da baima wasu irinta ba. Dole ne kafi wasu, sannan wasu ma su fika don ba yadda zai yuwa kowa ya zama iri daya.
In dai kai dan halal ne dole kana da mahassada dake ma hassada bisa wata ni’ima da Allah yana, kuma ita kanta hassadar sai wanda yakai ake yuwa, wanda bai kaiba ko ta kansa ba’a bi.
Don haka ƴan uwa ka lazamci karatun Alkur’ani da azkar din safe da yammaci in zaka iya ka haɗa da sallar dare ka kuma kame zuciyar ka, bakin ka da hannayenka a barin cutar da kowa to da izinin Allah haka za’a ganka a barka, sai kaga hassadar da ake ma ta zama taki zuwa ga nasara da cigaba rayuwarka.
Allah ka tsare mu sharrin matsubbata, ka tsaremu sharrin masu kambun baka dana ido, Allah ka tsare mu sharrin masu ƙulle-ƙulle, binne-binne da jefe-jefe, Allah ka tsare mu sharrin mutum da aljan.
Shehu Nasiru Muhammad, malami a Tsangayar Koyar da Ilimin Islama da ke Jigawa State College of Education and Legal Studies.