Home Wasanni Ba zan fasa yin Azumi ba saboda Tamaula – Mo Salah

Ba zan fasa yin Azumi ba saboda Tamaula – Mo Salah

0
Ba zan fasa yin Azumi ba saboda Tamaula – Mo Salah

Daga Abba Ibrahim Gwale

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Muhammad Salah ya bayyana cewa duk da cewa yanzu lokacin azumi ne kuma ga wasan karshe na cin kofin zakarun turai amma bazai kiyin azumi ba saboda kwallon kafa.

Salah ya bayyana hakane yayin wata hira da manema labarai a shirye shiryen da kungiyarsa ta Liverpool takeyi na buga wasan karshe na cin kofin zakarun turai da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a yau Asabar.

A kwanakin baya dai an bayyana cewa watakila dan wasan yakiyin azumi a ranar Asabar saboda wasan na karshe domin yasamu kwarin gwuiwa da kuma karsashi a wasan da zasu fafata.

Sai dai rahotanni daga kasar Masar wato Egypt sunce dan wasan zaici gaba da yin azumin nasa  har zuwa ranar wasan kuma zai fita yayi wasansa batare da rashin karfi ba kamar yadda ake tunani.

An bayyana cewa iyalan dan wasan dake kasar ta Masar sun shirya yanka dabbobi guda uku domin neman nasara da kuma taimakawa dan uwansu da addu’a a wasan da za’a fafata da kungiyar Real Madrid a filin wasa na Olympic dake babban birnin qasar Ukraine wato Kiev.

Liverpool dai tana neman lashe kofin karo na shida a tarihi yayinda ita kuwa Real Madrid take kokarin lashe kofin karo na 13 sannan kuma na uku a jere.