Home Kasuwanci Babban bankin Nijeriya ya rage adadin kuɗin da za a riƙa cire wa a banki da POS

Babban bankin Nijeriya ya rage adadin kuɗin da za a riƙa cire wa a banki da POS

0
Babban bankin Nijeriya ya rage adadin kuɗin da za a riƙa cire wa a banki da POS

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani sabon fasalin karbar kudi daga banki wanda ya gindaya cewar babu wani mutum da zai iya cire kudin da ya wuce naira dubu 100 daga banki a mako, yayin da kamfanoni kuma aka sanya musu ka’idar kada su wuce naira dubu 500.

Sanarwar da babban bankin kasar ya gabatar, yace babu wani mutum da zai iya karbar kudin da ya zarce sama da naira dubu 20 daga tashohin karbar kudaden da ake kira POS kowacce rana.

Babban bankin, ta hannu Haruna Mustafa, daraktan dake harkokin bankuna yace sakamakon kaddamar da sabbin kudaden da aka sauya fasali a ranar 23 ga watan Nuwamba da kuma shirinsa na mayar da hada hadar kudade ta bankuna da ake kira ‘cashless’, ya umurci duk bankunan kasuwancin kasar da kuma hukumomin dake hada hadar kudade da su tabbatar da amfani da sabon umurnin.

Sanarwar ta kuma ce daga wannan lokaci, bankuna ba zasu amince da cakin-kudin da ake baiwa mutane da ya wuce baira dubu 50 ba ga wani mutum, ko kuma naira miliyan 10 ga kamfanoni.

Babban bankin yace daga wannan lokaci, takardun kudaden naira 200 kawai za’a dinga zubawa a wuraren cire kudaden da ake kira ‘ATM’ domin baiwa jama’a damar cire naira dubu 20 kacal kowacce rana.

Bankin ya kuma baiwa bankunan kasuwanci umurnin karbar takardun shaidu daga jama’a masu karbar kudi da suka hada da katin shaidar zama ‘dan kasa da fasfo na tafiye tafiye da lasisin tuki da lambar shaidar da ake kira BVN da shaidar cire kudi da sanya hannun babban jami’in banki kafin fitar da kudin ko kuma rubutacciyar takardar amincewa a fidda kudin daga shugaban banki.

Babban bankin yace yana bukatar bankunan su dinga gabatar masa da cikakkun bayanai akan yadda mutane ke daukar kudin da suka wuce kima kowanne wata domin sanya ido akai.

Dama shugaban babban Bankin Godwin Emefiele yace yan najeriya zasu fuskanci matukar wahala wajen fidda kudi a banki lokacin da aka gabatar da sabon sauyin kudaden da akayi watan jiya.