
Kabiru Bayero, babban ɗan Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi baiko da ƴar wani fitaccen ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa a Jihar Sokoto, Alhaji Ummarun Kwabo.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa tuni manya da ga masarautar Kano da Bichi su ka sauka a Sokoto a jiya Asabar domin nemarwa Kabiru auren Aisha Ummarun Kwabo.
Manyan da su ka wakilci ango, a bisa jagorancin Wazirin Kano, Sa’ad Giɗaɗo, sun haɗa da Sarkin Dawaki Maituta Kano, Abubakar Bello Tuta; Dan Isan Kano, Kabiru Tijjani Hashim; Dandarman Kano, Bello Bayero da; Kachallan Kano, Magaji Galadima.
A gidan gwamnatin Jihar Sokoto a ka yi taron baikon, inda tsohon gwamnan jihar, Attahiru Bafarawa ya wakilci dangin amarya.
Wazirin Sokoto, Sambo Junaidu, shine ya wakilci Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar.
Wakilan angon sun miƙa N250,000 a matsayin sadaki.
Kabiru ya kammala digirin sa a fannin harkar kasuwanci, wato “Business Administration.”