
Jam’iya mai mulki ta APC ta fara sayar da fama-faman ƴan takarar shugabancin jam’iya a babban taron da za a ta yi ranar 26 ga watan Maris.
Shugaban Matasa na Ƙasa na riƙon ƙwarya, Ismail Ahmed ne ya baiyana hakan ga manema labarai a Abuja a jiya Talata bayan fitowa da ga wata ganawar sirri.
Ahmed ya ce kwamitin ne ya ɗora masa alhakin sanar da fara sayar da fama-faman na dukkanin gurabe, har da ma na shiyya-shiyya da kuma na ƙasa baki ɗaya.
Ya ce kwamitin ƙoli na jam’iyar ta amince da sayar da fom ɗin shugaban jam’iya na ƙasa kan Naira miliyan 20, sai kuma na sakataren jamiya na ƙasa da na Mataimakin Shugaban Jam’iya na Ƙasa, shiyyar kudu da arewa da za a sayar da shi kan Naira miliyan 10.
Ahmed ya ƙara da cewa fim ɗin duk wani gurbi a kwamitin ƙoli, za a sayar da shi Naira miliyan 5.
Sai kuma fim ɗin duk wani gurbi a kwamitin zartaswa na ƙasa, za a sayar da fom ɗin sa kan Naira miliyan 1.
Ya ce dukkanin wasu gurabe a bangaren shiyya, banda na Mataimakin Shugaban Jam’iya na Ƙasa, za a sayar da fom ɗin sa Naira dubu 500.
Ahmed ya ƙara da cewa za a sayar wa da mata da masu nakasa fom ɗin ko wanne gurbi kan kashi 50 na kuɗaɗen da a ka sanya.