Home Labarai Babban taron APC: Gwamnan Nassarawa ya mayar da Naira miliyan 20 da ta yi ragowa a kwamitinsa

Babban taron APC: Gwamnan Nassarawa ya mayar da Naira miliyan 20 da ta yi ragowa a kwamitinsa

0
Babban taron APC: Gwamnan Nassarawa ya mayar da Naira miliyan 20 da ta yi ragowa a kwamitinsa

 

 

 

 

 

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Babban Taron Jam’iyyar APC, ya mika rahoton kwamitin.

Gwamna Sule, a lokacin da yake mika rahoton ga shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu a sakatariyarta ta kasa a yau Juma’a a Abuja, ya kuma maido da kuɗaɗen da su ka yi ragowa a cikin kuɗaɗen da kwamitin ya kashe har Naira miliyan 20 ga asusun jam’iyyar.

Sakataren kwamitin, Bello Mandiya da sauran mambobinsa sun halarci wajen mika rahoton.

Da yake gabatar da cikakken rahoton, Sule ya ce an ba kwamitin Naira miliyan 140 domin gudanar da ayyukansa, amma ya kashe Naira miliyan 120 kawai.

“Da farko an ba mu Naira miliyan 30 a rana guda bayan kaddamar da mu, daga nan sai muka sake samun Naira miliyan 60. Gaba daya jam’iyyar ta ba mu Naira miliyan 140.

“Ga ni na zo da ceki na Naira miliyan 20 don gabatar wa shugaban jam’iyyarmu a matsayin adadin da ya rage daga abin da aka ba mu, saboda ba duka mu ka kashe ba,” in ji Sule.

Adamu, a nasa jawabin, ya ce an yaba da matakin gaskiya da jajircewar da kwamitin ya nuna.

Ya ce kwamitin ya yi aiki mai kyau kuma ya yi gaskiya da rikon amana har ya kai ga bayyana wasu rarar abin da ya zama misali mai kyau.